Kawance yayi rana: Gwamnatin kasar Amurka zata aiko ma Najeriya jiargen yaki 12 da dimbin makamai

Kawance yayi rana: Gwamnatin kasar Amurka zata aiko ma Najeriya jiargen yaki 12 da dimbin makamai

Gwamnatin kasar Amurka ta kammala shirye shiryen aiko ma Najeriya manyan jiragen yaki na zamani guda 12, kirar Tucano, tare da dimbin makamai masu sarrafa kansu kamar yadda cinikayya tsakanin kasashen biyu ta kullu.

Premium Times ta ruwaito Najeriya ta siya jiragen ne daga kasar Amurka da nufin yaki da yan ta’addan Boko Haram da ma sauran barazanar tsaro da kasar ke fuskanta, da suka hada da rikicin makiyaya da manoma da sauransu.

KU KARANTA: Iyayen yan matan Chibok sun mutu a wata mummunan hadarin Mota

Shi ma shugaban ofishin jakadancin Amurka a Najeriya ta tabbatar da cinikayyar, inda yace tuni Najeriya ta biya kudaden jiragen da na sauran makaman, kudin da suka haura dala miliyan 400.

Kawance yayi rana: Gwamnatin kasar Amurka zata aiko ma Najeriya jiargen yaki 12 da dimbin makamai
Jirgin Yaki

Baya da jiragen yaki, makaman da Najeriya ta siya daga wajen Amurka sun hada da bamabamai, bindgu amsu sarrafa kansu, roka roka, na’urorin leken asiri da dai sauransu, kamar yadda majiyar Legit.ng ta ruwaito.

Kamfanin Pratt&Whitney Canada ne suka kera jirgin Super Tucano, kuma farashin jirgin yakin ya haura dala miliyan 10, yayinda na’urorin leken asirin suka fito daga kamfanin Embraer na kasar Brazil.

Daga karshe jami’in difomasiyyar ya tabbatar da gayyatar da shugaban kasar Amurka Donald Trump yayi ma shugaban kasa Muhammadu Buhari zuwa fadar gwamnatin Amurka, White House da nufin tattaunawa, wanda hakan ya sanya shi zama shugaban kasar Afirka na farko da ya fara ziyartar White House.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng