Gyara kayan ka ba sauke mu raba ba: ‘Dan a-mutun Buhari ya aika masa budaddiyar wasika
Mun kawo maku abubuwan da Simon Kolawole ya rubuta a budaddiyar wasikar sa da ya aika zuwa ga Shugaba Buhari a karshen wannan makon. Simon Kolawole ya fadawa Shugaban kasar cewa sai yayi da gaske.
1. A sallami wasu Ministoci
Simon Kolawole ya nemi Shugaba Buhari ya sallami wasu mukarraban sa da Ministocin Gwamnatin wanda ba su da amfani. Kolawole yace tun ba yau ba ya kamata ace an kora wasu don ba su cancan aiki da Gwamnatin ba.
2. Garambawul a gidan Soja
‘Dan Jaridar yace akwai matsala sosai tsakanin manyan Hafsun Sojin kasar inda har ta kai wasu manyan Sojojin ba su magana da juna don haka ya nemi Shugaba Buhari ya dauki mataki kan wannan domin kasa ta zauna lafiya.
KU KARANTA: Sojojin Najeriya sun yi ram da Matan ‘Yan Boko Haram a Borno
3. Yaki da barna da rashin gaskiya
Bayan nan kuma Kolawole yace ba shakka marasa gaskiya na kokarin dawo da hannun agogo baya amma Shugaban kasar ya rike wasu marasa gaskiya a Gwamnatin sa wanda da kyar ma ta sa aka kori irin su Babachir Lawal. Bayan nan dai ana ta takun saka tsakanin EFCC da DSS, NSA da NIA, dsr.
4. Rikicin Makiyaya
Kolawole yace daga cikin inda aka samu sakaci wajen Shugaban kasar akwai rikon da yayi wa rikicin Makiyaya da yayi sanadiyyar rayuka. Marubucin ya nemi Shugaban kasar ya tashi tsaye haikan a wannan bangare.
5. Sukar matasa
A karshen Marubucin yayi tir da jawabin da Shugaban kasar yayi game da Matasan kasar nan da lalacin su lokacin da ya ke halartar wani taro a Landan.
Marubucin yace tattalin arziki na bunkasa bayan abubuwa sun tabarbare da farko sannan kuma Gwamnatin na kokari wajen gina hanyoyi a kasar ya kuma ce har gobe Shugaba Buhari mutum ne mai amana.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng