Magoya bayan Buhari a Arewacin Najeriya sun gamu da cikas wajen wani taro

Magoya bayan Buhari a Arewacin Najeriya sun gamu da cikas wajen wani taro

- Jam’iyyar APC ta tashi wani taro baram-baram ba yadda aka so ba

- ‘Yan iskan gari sun hana ana yi taron siyasan da aka shirya a Jigawa

- Wani ‘Dan Majalisa yayi wa Gwamnan na Jigawa mubaya’a kan 2019

Dazu mu ka samu labari cewa wasu ‘Yan iskan gari sun tarwatsa taron da ‘Yan Jam’iyyar APC a Arewacin Najeriya su ka shirya domin nuna goyon bayan su ga Shugaba Muhammadu Buhari da kuma Gwamna Abubakar Badaru.

Masu goyon bayan Shugaban kasa Buhari da kuma Gwamnan Jihar Jigawa Abubakar Badaru a zabe mai zuwa na 2019 sun shirya wani gangami a Arewa-maso-yammacin Jihar Jigawa. Sai dai haka aka tashi taron baram-baram.

Magoya bayan Buhari a Arewacin Najeriya sun gamu da cikas wajen wani taro
Gwamnan Jigawa Badaru zai gamu da kalubale a 2019

Shugaban Jam’iyyar APC na Jihar Jigawa Ado Kiri bai samu damar yi wa dinbin magoya bayan su jawabi ba bayan da wasu tsageru su ka tada zaune tsaye, su na sukar Sanata Abdullahi Gumel na Yankin wanda a boye ya shigo taron.

KU KARANTA: Sanatocin PDP Saraki yayi amfani da su ya dakatar da Ndume

Jaridar Premium Times tace tsohon Sanatan Jihar Danladi Sankara ne ya shigo da Sanata A. Gumel a boye gudun ‘yan iskan gari su yi masa lahani. Taron dai ya tashi ‘Yan Majalisa 2 ne kurum na Jihar su ka halarci wannan babban taro.

‘Dan Majalisar Garki/Bubura Adamu Fagen Gawo ya bayyana cewa su na bayan Gwama Badaru ya sake takara a 2019. Sauran wadanda su ka halarci taron sun hada da tsohon Mataimakin Gwamna Ahmed Mohammed da Isa Gerawa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel