Sojojin Najeriya sun yi ram da manyan ‘Yan Boko Haram 2 a Borno

Sojojin Najeriya sun yi ram da manyan ‘Yan Boko Haram 2 a Borno

- Wasu ‘Yan ta’addan Boko Haram sun sallamawa Sojojin Najeriya

- Akwai manyan Sojojin Shekau da su ka saduda a cikin Jihar Borno

- Daga ciki kuma akwai iyalin wani babba cikin Sojan ‘Yan ta’addan

Dazu nan mu ka samu labari daga Jaridar The Cable cewa Rundunar Sojin Najeriya sun samu gagarumar nasara kan ‘Yan ta’addan Boko Haram bayan da wasu Sojoji su ka mika kan su da kan su hannun Jami'an tsaro.

Sojojin Najeriya sun yi ram da manyan ‘Yan Boko Haram 2 a Borno
Sojojin Najeriya sun samu nasara kan 'Yan Boko Haram

Wasu manyan Sojoji 4 na bangaren Abubakar Shekau ne su ka sallama su ka mika kan su gaban Rundunar Sojojin kasar a barikin Sojan da ke Maimalari inji wani babban Jami’in Sojan kasar da ke filin daga Birgediya Janar Oneyama Nwachuwku.

KU KARANTA: 'Yan Sanda sun kashe wani babban 'dan ta'adda a Akwa-Ibom

Wasu ‘Yan ta’addan da Shekau ya ke ji da su ne su ka tuba a hannun Rundunar Sojin Najeriya na Operation Lafiya Dole a Barikin Maimalari da ke Maiduguri cikin Jihar Borno. ‘Yan ta’addan sun kunshi maza 3 ne da mace 1 da kuma yara 3.

Daya daga cikin wanda aka kama Likita ne na Sojojin. Macen da ta shiga hannu kuma matar daya daga cikin wani babban Sojan na Boko Haram sannan kuma yaran 2 daga ciki ‘Ya ‘yan babban Sojan ta’addan ne kamar yadda aka bayyana mana.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel