Hukumar Sojin Najeriya ta fito da sabon atisaye don murkushe Boko Haram

Hukumar Sojin Najeriya ta fito da sabon atisaye don murkushe Boko Haram

Hukumar Sojin Najeriya ta bayar da sanarwan kaddamar da wata sabuwar atisaye na musamman wanda zai murkushe yan ta'addan Boko Haram baki daya. A cewar shugaban bayar da horo da ayyuka na hukumar, David Ahmadu, za'a shafe watanni hudu ana gudanar da atisayen.

A dalilin atisayen da akayi wa lakabi da "Operation Last Hold" hukumar soji zata karo battaliyan soji guda shida tare da wasu muhimman kayayakin yaki kamar yadda Manjo Janar Ahmadu ya sanar.

Kimanin mutane 100,000 ne suka rasa rayyukansu sakamakon ayyukan ta'adanci da yan kungiyar na Boko Haram suka rika kwararowa a jihohin Yobe, Adamawa da Borno dake yankin Arewa maso gabashin Najeriya tun daga shekarar 2009.

DUBA WANNAN: Lafiya dole: Wasu mayakan kungiyar Boko Haram sun saduda, sun mika wuya ga sojojin Najeriya

A baya, hukumar Sojin Najeriya ta sanar da cewa ta karya lagwan kungiyar na Boko Haram ma'ana fizge-fizgen mutuwa ne kungiyar keyi sai dai duk da hakan, kungiyar ta cigaba da kai sabbin hare-hare a kan fararen hula har ma da sojojin.

A bangarensa, Mr Chukwu, yace wannan sabon atisayen da za'a fara zai tabbatar da cewa an murkushe kungiyar baki daya ta hanyar lalata dukkan sansanoninsu da kuma inda suke zama a tafkin Chadi.

Ya kuma kara da cewa wannan atisayen zai tabbatar da ceto dukkan mutanen da kungiyar na Boko Haram ke garkuwa da su. An kaddamar da wannan atisayen ne bayan na farko wanda akayi wa lakabi da "Lafiya Dole"

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel