'Yan bindiga sun sake ta'adi a Zamfara, sun kashe mutane 20
Yan fashin da makami sun kashe a kalla mutane 20 a wani hari da sukakai a Kabaro da Danmani a karamar hukumar Maru dake jahar Zamfara kamar yadda muka samo daga jaridar Daily Trust.
A satin daya gabata maharan sunkai hari mai kama da wannan a garin Kuru-kuru da Jarkuka a karamar hukumar Anka inda suka kashe mutane 26.
Harin da akakai a Kabaro an taba kai kwatankwacin sa shekaru 6 da suka wuce inda aka kashe mutane 18 da kuma makiyaya. Sannan irin hakan ya taba faruwa a watan Octoban 2012.
DUBA WANNAN: An saka ladan N500,000 a kan 'yan bindiga da suka kashe dan sanda a caji ofis
Rikicin daya faru a Dansadau yana daya daga cikin hari mafi muni da yan fashin da kuma makiyaya sukakai a yankin wanda ke kusa da Inda aka kashe jagoran su kungiyar masu fashi da satan shanu da akafi sani da Buharin daji a Dansadau.
Wasu mazauna garin sun shaidawa Daily Trust cewa maharan sun kashe wasu mutane biyu akan babur akan hanyarsu ta zuwa garin kuma hakan yasa mutane garin suka tinkiri yan bindigar inda aka kashe mutane 20 cikinsu saboda makaman yan bindigan sunfi karfi.
Me magana da yawon kwamandan yan sanda DSP Muhammad Shehu ya tabbatar da afkuwar lamarin saidai bai bayyana adadin asarar da aka samu ba.
Kwamandan dake kula da yankin da kuma DSP da kuma hukumar tsaro sun halarci gurin domin duba halin da ake ciki.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng