Okorocha ya dorawa duk wani baligi dake jihar Imo harajin N3000

Okorocha ya dorawa duk wani baligi dake jihar Imo harajin N3000

- Gwamna Rochas Okorocha na jihar Imo ya bullo da wata sabuwar haraji a jihar wanda za'a rika amfani da kudin wajen ayyukan cigaba

- Gwamnatin na bukatar a kalla baligai 2000 daga gundumomi 637 da ke jihar su rika biatn harajin N3000

- Gwamnan yayi barazanar dakatar da albashi masu sarautun gargajiyan da al'ummar garuruwansu suka ki biyan harajin

Gwamnar jihar Imo Rochas Okoracha, ya sanya wa duk wani baligi a jihar haraji na N3000 wanda za'a rika amfani dashi wajen gudanar ayyukan cigaba da more rayuwa a jihar kamar yadda jaridar Daily trust ta ruwaito.

A wata sanarwa mai dauke da sa hannun kwamishinan raya garuruwa da al'adu na jihar, Louis Doru, ya bayyana cewa za'ayi amfani da kudin wajen ayyukan taimakon kai-da-kai ne a jihar.

Okorocha ya dorawa duk wani balagege dake jihar Imo harajin N3000
Okorocha ya dorawa duk wani balagege dake jihar Imo harajin N3000

DUBA WANNAN: An gano sunan dalibar da suka yi waya da Farfesa mai rabon maki bayan lalata

Duro yace gwamnatin tayi wa akallah mutane 2,000 rigista a kowane garuruwa 637 masu cin gashin kansu. Ya kara da cewa za'a daura alhakin karbar kudaden kan wasu garuruwa da aka amince dasu kuma ana sa ran kowannensu zasu biya a kallah naira miliyan shida.

Okorocha kuma yayi gargadin cewa gwamnati zata dakatar da albashin Sarakunan gargajiya da al'ummar garuruwansu suka ki bayar da hadin kai wajen biyan harajin.

"Domin saukakawa wajen biyan kudin gwamnatin tayi amfani da hukumar CGC tun a watan Satumban 2016 inda za'ayi rigista da kungiyar wanda take neman a kalla balagaggu 2000 daga kowane gari", inji sanarwan.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164