Hannun biri: Wani matashi ya lakada ma Likita dan banzan duka kan yayi ma matarsa aiki, ko me yayi zafi?
Wani matashi ya kai hankali nesa inda ya lakada ma wani babban Likita dukan tsiya, bayan matarsa ta mutu a sakamakon aikin tiyata da likitan yayi mata, inda yace likitan bai nemi izininsa ba, kamar yadda Aminiya ta ruwaito.
Majiyar Legit.ng ta ruwaito matashin mai suna Abdulkadir Abubakar dan asalin garin Zangon Kataf na jihar Kaduna yana fadin cewa nakuda ne ta taso ma matarsa, Hajara, ganin halin da ta shiga ne ya sanya shi garzaya da ita zuwa babban Asibitin garin Zangon Kataf.
KU KARANTA: Aikata baɗala a gidajen kallon kwallo: Sarkin Kano ya baiwa Daurawa muhimmin aiki
Sai dai ma’aikatan jinyar da suka tarar a Asibitin basu da kwarewa duba matar, sa’annan kuma likitan da ya kamata ya duba ta ya kulle kofarsa, sun yi ta bugawa masa kofa bai bude ba, daga nan ne sai Abdulkadir ya garzaya da Hajara zuwa babban Asibitin garin Kafanchan.
Zuwansu Kafanchan sai aka bayyana musu Hajara na bukatan karin jini, amma ganin cewa ta kwana biyu bata sanyo komai a bakinta ba, sai Mijin nata ya bata ruwan shayi ta sha, daga nan kuma shi da kaninsa suka nufi inda ake gwada jini don dibar jininsu a kara mata.
Maigidan Hajara yace: “Mun dawo daga inda aka gwada jinin namu ne sai bamu tarar da Hajara a dakin da muka barta ba, aka fada mana wai an shiga da ita tiyata, kuma babu wani cikin yan uwana da ya bada wannan izini, can sai wani likita ya fito ya shaida mana wai Hajar ta mutu sakamakon shayin da muka bata.”
Daga nan ne fa Abdulkadir ya rarumi Likitan ya damfara da shi da kasa, sakamakon tsananin bacin rai da yake fama da shi a wannan lokaci. “Gaskiya ba’ayi min adalci ba, ya za’ayi su yi mata aikin tiyata ba tare da izini ba, kuma su ce min wai shayin da na bata ne ya kashe ta, bayan su suka amince na bata ta sha?” inji shi.
Ango Abdulkadira yace ya bar komai a hannun Allah, sai dai duk kokarin da majiyarmu tayi na jin ta bakin shugaban Asibitin, Dakta Jonathan Gajere don samun karin bayani game da lamarin ya ci tura.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng