Karshen alewa kasa: Sojojin Najeriya sun cafke masu shirya kashe kashen da ake yi a jihar Taraba

Karshen alewa kasa: Sojojin Najeriya sun cafke masu shirya kashe kashen da ake yi a jihar Taraba

Rundunar Sojin Najeriya ta cika hannu da wasu mutane da take zargin sune masu rura rikicin jihar Taraba tare da kitsa duk kashe kashen da ake yi a jihar, kamar yadda jaridar Aminiya ta ruwaito.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Kaakakin rundunar Sojin kasa,Birgediya Texas Chukwu ne ya sanar da haka, inda yace dakarun rundunar sun kama mutanen ne a ranar Juma’a 13 ga watan Afrilu, inda ya bada sunayensu kamar haka: Mista Danjuma da Mista Dan-Asabe Gasama.

KU KARANTA: Rikicin jihar Taraba: Sojojin Najeriya sun kama wani kasurgumin dan bindiga a Taraba

Texas yace an kama mutanen biyu ne da hannu cikin tada zauni tsaye tare da shirya kashe kashe a karamar hukumar Takum da Ussa dake jihar, bayan wasu bayanan sirri da rundunar ta samu game da ayyukan mutanen biyu.

“Sakamakon samun bayanan sirri da rundunar Soji ta yi, mun kama wasu mutane guda biyu dake shirya tsare tsaren kai ma Fulani hari da yi musu kisan kiyashi, da sauran kabilun yankin jihar Taraba.” Inji Kaakakin.

Sai dai wasu rahotanni sun bayyana cewa gwamnan jihar Taraba ya bukaci rundunar Sojojin Najeriya dasu gaggauta sakin mutanen biyu, inda ya wanke su daga aikata duk wani laifi, tare da zargin Sojojin da nuna bambamci da son kai a aikin tabbatar da tsaro a jihar Taraba.

Amma a martanin da ya mayar ga zargin da gwamnan yayi, Texas Chukwu ya musanta zarge zargen, inda yace rundunar Sojin Najeriya bata goyon bayan wani addini ko kabila a aikin da suke na magance ayyukan miyagun mutane.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel