Gwamnatin Buhari ta gaza maida amsoshin tambayoyin da wani Lauya yayi mata

Gwamnatin Buhari ta gaza maida amsoshin tambayoyin da wani Lauya yayi mata

Kun ji cewa babban Lauyan Najeriya Femi Falana yayi wa Gwamnatin Buhari wasu tambayoyi game da tallafin man fetur wanda har yanzu karamin Ministan fetur na kasar Ibe Kachikwu bai maida martani ba.

Ga dai tambayoyin da aka aikawa Gwamnatin Buhari nan kamar haka:

Gwamnatin Buhari ta gaza maida amsoshin tambayoyin da wani Lauya yayi mata
Femi Falana yayi wa Gwamnatin Buhari tambaya kan tallafin man fetur

1. Karin gangar man fetur da ake sha

A bara Najeriya na shan lita miliyan 28 ne na fetur kullum, sai kuma ga shi yanzu NNPC na cewa a duk rana Najeriya na shan sama da lita miliyan 50 na man fetur. Dalilin haka ne kudin tallafi ya tashi har zuwa Miliyan 726 a kowace rana. Falana yace ta ya man da ake sha ya karu haka kwatsam?

KU KARANTA: An bada umarni a duba lamarin da ya ja aka sungume sandar Majalisa

2. Satar mai zuwa wasu kasashe

Lauyan yace a kaddara duk rana ana sace gangar mai har lita 250, 000 zuwa kasashen Makwabta, yace duk da haka babu yadda za ayi hakan yayi sanadiyyar karuwar abin da Najeriya ke sha da sama da lita miliyan 30. Falana ya kuma nemi ya ji dalilin da ya sa ake karkatar da mai har yanzu.

3. Cinikin man da Najeriya ke yi

Haka kuma Lauyan yace Gwamnatin Buhari ta ki bayyanawa jama’a abin da aka samu da aka saida sama da litan mai har miliyan 600 a kan farashi N145 kwanakin baya. Bayan nan kuma NNPC a gida ta tace ganga kusan 500, 000 amma har gobe ba a san inda kudin su ka shiga ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng