Rahoton korar sabbin malaman makaranta 4,500: Gwamnatin jihar Kaduna ta mayar da martani

Rahoton korar sabbin malaman makaranta 4,500: Gwamnatin jihar Kaduna ta mayar da martani

A yau, Alhamis, ne gwamnatin jihar Kaduna ta mayar da martani a kan rahoton cewar ta kori mutum 4,500 daga cikin sabbin malaman makarantar da ta dauka aiki.

A jiya ne rahotanni suka mamaye kafafen yada labarai cewar gwamnatin jihar Kaduna ta sallami malaman makaranta 4,500 daga cikin fiye da malaman makaranta 11,000 da ta dauka aiki satin da ya wuce.

A wata sanarwa da kakakin gwamnan jihar Kaduna, Samuel Aruwan, ya sanyawa hannu, gwamnatin jihar Kaduna ta ce rahoton ba gaskiya bane.

Rahoton korar sabbin malaman makaranta 4,500: Gwamnatin jihar Kaduna ta mayar da martani

Gwamnatin jihar Kaduna ta mayar da martani

Sanarwar ta kara da cewa gwamnatin jihar Kaduna bata kori malami koda guda daya ba daga cikin sabbin malaman makarantar data dauka aiki ba. Gwamnatin ta bukaci jama'a da su yi watsi da rahoton domin zuki tamalle ce kawai.

DUBA WANNAN: Dalilin ganawa ta da Osinbajo bayan tashin hankali a majalisar dattijai

Sanarwar ta kara yin albishir din cewar gwamnatin jihar Kaduna zata sanar da jadawalin aikin sake daukan wasu sabbin malaman makarantar 13,605 karkashin hukumar ilimin bai daya (SUBEB) ta jihar.

An sha cece-kuce bayan gwamnatin jihar kaduna ta sallami makaranta fiye da 20,000 bayan sun gaza cin jarrabawar gwaji da gwamnatin jihar tayi masu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel