Babu ruwan soyayya da yare ko kabilar mutum Inji Diyar Ganduje

Babu ruwan soyayya da yare ko kabilar mutum Inji Diyar Ganduje

- Kwanaki 'Diyar Ganduje ta auri wani yaron Gwamnan Jihar Oyo

- Duk da tana Bafullatana ce ta auri Bayarabe takwaran ta kwanaki

- Fatima Ganduje tace har ta fara koyon abubuwa a yaran yarbanci

'Diyar Gwamnan Jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje watau Fatima mai shekara 24 a Duniya da ta auri Idris Ajimobi ta bayyana yadda ta hadu da Sahibin ta a wata hira da ta zo mana daga Information Nigeria.

Babu ruwan soyayya da yare ko kabilar mutum Inji Diyar Ganduje

Diyar Ganduje tace tana matukar kaunar mijin ta

Fatima Abdullahi Umar Ganduje ta bayyana cewa ta sanadiyyar wani a dangin ta ne ta hadu da Idris Abiola Ajimobi. Allah kuma ya sa akwai rabo don su na haduwa sai abubuwa su ka mike shar. Fatima tace Mijin ta mutum ne nagari.

KU KARANTA: Osinbajo yayi kira ga Matasa su tashi tsaye a siyasance

'Diyar Ganduje wanda tayi karatun ta a Jami'ar Amurka ta Najeriya da ke Yola tace duk da Mijin ta Bayarabe ne yayin da ita kuma ta ke Bafullatana, abubuwa su na tafiya lafiya lau tsakanin su inda ta ke kayan yare da abincin Yarbawa.

Wannan Baiwar Allah ta yabawa 'Yan uwan Mijin na ta da surukar ta watau Mai dakin Gwamna wanda tace sun rike ta hannu biyu-biyu. Ganduje tace ba za ta iya samun 'yanuwan Mijin da su ka fi su ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel