Tallafin man fetur: An hurowa Gwamnatin Shugaba Buhari wuta

Tallafin man fetur: An hurowa Gwamnatin Shugaba Buhari wuta

- Kudin da Najeriya ta ke biya kan tallafin man fetur yayi ‘dan-karen tashi

- Wani Lauya a Najeriya ya nemi Gwamnatin Buhari tayi wa mutane bayani

- Lauyan babu yadda za ayi a rika biyan tallafin sama da Tiriliyan a shekara

Kwanaki mu ka samu labari cewa Gwamnatin Shugaba Buhari ta kashe abin da ya haura Naira Tiriliyan guda wajen tallafin man fetur don haka ne wani babban Lauya ya taso Gwamnatin a gaba. Falana ya musanya rahoton da NNPC ta saki.

Tallafin man fetur: An hurowa Gwamnatin Shugaba Buhari wuta
Femi Falana ya musanya rahoton Kamfanin NNPC na mai

Femi Falana wanda babban Lauya ne a kasar nan ya ba Gwamnatin Shugaba Buhari mako daya tal yayi jama’a bayanin kudin da aka kashe a kan tallafin man fetur daga karshen shekarar bara zuwa watan Jiya na Maris a Najeriya.

KU KARANTA: An jefa na hannun-daman Shugaba Buhari a gidan yari

A bara NNPC tayi ikirarin cewa a kullum ana amfani da lita miliyan 28 na fetur wanda hakan ke nufin ana biyan ‘yan kasuwa kudin tallafi na Miliyan 726 a kullum. Sai dai yanzu a bana an ce man da ake sha a Najeriya ya haura lita miliyan 50.

Lauyan yace akwai abin dubawa a bayanin na Hukuma ganin yadda kudin da ake biya domin tallafin yayi wani tashin gauron-zabo. Falana ya aika takardar sa ne ga karamin Ministan man fetur Ibe Kachikwu inda ya nemi ayi ke-ke-da-ke-ke.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel