Kuma dai: Yan bindiga suna fantsama jihar Filato sun bindige mutum 4 har lahira
Rundunar Yansandan jihar Filato ta sanar da mutuwar wasu mutane guda hudu a karamar hukumar Bassa a ranar Laraba 18 ga watan Afrilu a hannun wasu yan bindiga da har yanzu ba’a gane ko suwanene ba, inji rahoton Premium Times.
Majiyar Legit.ng ta ruwaito Kaakakin rundunar Yansandan jihar, Terna Tyopev yana cewa jami’an Yansanda sun yi kokarin cafke yan bindigar ta hanyar bin sawunsu, amma aikin gama ta gama.
KU KARANTA: An kashe maciji ba’a sare kansa ba: Yaran Buharin Daji sun hallaka wasu mutane 2 a jihar Zamfara
“Yan bindigan sun far ma mutanen ne ba jib a gani, inda suka kashe Adamu Sunday mai shekaru 38, Jatau Akus mai shekaru 39, Chohu Awarhai da Marcus Mali dukkaninsu masu shekaru 22, amma tuni muka mika gawarwakinsu zuwa Asibitin kwararru na jihar Filato.” Inji Kaakakin
Kaakaki Tyner ya bayyana cewa yan bindigan sun kashe mamatan ne a unguwar Rogo DTV dag garin Bassa, sai dai jama’a na ganin kisan baya rasa alaka da rikicin makiyaya da manoma da ya dabaibaye yankin jihar.
A wani labarin kuma, wasu yan bindiga da ake zargin makiyaya ne sun hallaka wasu mutane biyu a jihar Zamfara, ta hanyar yi musu kisan wulakanci, inda suka yi ma guda yankan rago bayan sun harbe shi, sa’annan suka murde ma guda wuya, sakamakon bindiga bata shigarsa.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng