Gwamnatin tarayya ta roki ma'aikatan lafiya su janye yajin aikin da suka tafi
- Gwamnatin tarayya ta roki hukumar lafiya ta janye yajin aikin data tafi
- Wannan roko ya fito ne daga bakin Ministan Lafiya, Dr Chris Ngige
- Ministan yace yayi mamakin yadda kungiyar na ma'aikatan lafiya ta tafi yajin aikin duk da kokarin da gwamnati tayi na cika alkawuran data dauka
Ministan lafiya Dr Chris Ngige ya roki hukumar data janye yajin aikin da ta tafi, yayi wannan rokon ne a ranar laraba data gabata a Abuja. Ngige yace yayi mamakin yanda hukumar ta take yarjejeniyar da suka kulla a watan satumba shekarar 2017.
A rubuce yake cewa gwamnatin tayi kokari wajen cika dukkan wasu bukatu na Kungiyar wanda ya harda da biyan dukkanin wasu bashi, karancin biyan albashi a wasu bangarorin wanda aka zartar da yarjejeniyar a 30 ga satumba 2017.
DUBA WANNAN: Sarkin Daura ya roki shugaba Buhari ya sake duba batun Peace Corp
Gwamnatin tana rokon JOHESU da suyi duba ga marasa lafiyan dake kwance a asibitoci. A nasa bangaren yace gwamnati ba zata gaza ba wajen kula da marasa lafiyan dake kwance a asibito cin gwamnati inda su kuma ma'aikatan lafiyan suka ajjiye aiki. yana fata jehosu suyi duba da hakan.
Idan har hukumar lafiya taci gaba da wannan yajin aikin tofa gwamnati zatayi duba zuwa ga dokokin ma'aikata musamman section 43 Cap.T8 na dokokin gwantin jahar(LFN) 2014, wanda yai daidai dana imternational labour organization (ILO) na ka'idojin tafiya yajin aiki.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng