Basabamba: Wani Dan majalisa ya koma makaranta don koyar da dalibai Kurame (Hotuna)

Basabamba: Wani Dan majalisa ya koma makaranta don koyar da dalibai Kurame (Hotuna)

- Dan Majalisar dokokin jihar Jigawa ya koyar da dalibai Kuramai

- Dan Majalisar yayi alkawarin tallafa ma makarantar don cigaban ilimi

Wani dan majalisar dokokin jihar Jigawa, Aliyu Ahmed Aliyu dake wakiltar karamar hukumar Kirikasanm ya koma aji, inda ya shiga makarantar Kurame dake garin Hadejia ya koyar dasu karatu.

Rariya ta ruwaito Shugaban makarantar ne ya gayyaci Honorabul Aliyu don ganin ma kansa yadda suke gudanar da koya da koyarwa a makaranta, inda daga nan shima dan majalisar ya fada aji, inda aka hange shi yana biya ma daliban darasi.

KU KARANTA: Yawanci matasan Najeriya basu son karatu, sun fi kaunar zaman kashe wando – Buhari daga Landan

Basabamba: Wani Dan majalisa ya koma makaranta don koyar da dalibai Kurame (Hotuna)
Aliyu

Majiyar Legit.ng ta ruwaito suma daliban makarantar sun bukaci gwamnatin jihar Jigawa da ta bullo da darussan da za’a dinga koyar dasu sana’o’in hannu, domin suma su dogara da kansu bayan kammala karatunsu.

Bayan sauraron korafe korafen Malamai da daliban makarantar, Honorabul ALiyu ya yaba da kokarin da Malaman da ma na Daliban, inda yayi musu alkawarin tallafa musu don ganin sun samu ilimi cikin kwanciyar hankali.

Basabamba: Wani Dan majalisa ya koma makaranta don koyar da dalibai Kurame (Hotuna)
A ajin

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel