Yadda ake sace maza a yi masu auren dole a kasar Indiya
A wani lamari da zamu iya kwatanta shi da fadin nan na Bahaushe dake cewa, "Allah daya gari ban-ban, maza a kasar Indiya sun koka a kan yi masu auren dole.
A kasar Indiya dai dama mata ne ke biyan sadakin sure, sabanin yadda abin yake a nan Najeriya da ma wasu kasashen duniya.
Duk lokacin da aure ya mutu a Indiya, matar kan nemi miji ya dawo mata da sadakin da ya biya.
Yanzu dai ta kai matakin da maza a kasar Indiya ke fuskantar tursasa su yin aure, dalilin da ya saka su kokawa bisa kuncin da ake jefa rayuwar su.
Wani matashi, Roshan, dan shekara 17, ya ce an sace shi a bara an tilasta masa auren wata. Saidai daga bisani ya tsere ya bar matar tunda ba da son ransa ta aure shi ba.
DUBA WANNAN: Jerin sunayen matasan da suka kai hari majalisar dattijai suka dauke sandar majalisa
Wani mutum, Praveen Kumar, ya bayyana yadda aka sace shi a shekarar 2012 tare da tilasta shi auren matar sa, Maharani, wacce yanzu suke da yara da uku duk da a farko saida ya shafe shekaru uku ba ya kula matar.
Farfesa Bharati Kumar, wata malamar jami'a, ta ce wannan al'ada na da alaka da addini kuma iyaye na yin hakan ne domin kwadayin hada zuri'a da mazan da suka fito daga babban gida ko suke da wata nasaba.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng