Duba Jerin sunayen mutanen da suka shiga majalisar dattijai suka sace sandar majalisa
A yau ne aka samu wani hargitsi a zauren majalisar dattijan Najeriya bayan da wasu mutane biyar karkashin Sanata Omo Agege suka sace sandar majalisar.
Ana tsaka da zaman majalisar ne Sanata Omo Agege, da majalisar ta dakatar bisa adawar sa da kudirin majalisar na canja jadawalin zaben 2019, ya jagoranci wasu 'yan bangar siyasa suka yi kutse cikin zauren majalisar.
Rahotanni sun bayyana cewar ba a san ko su waye mutanen da Omo Agege ya saka suka sace sandar majalisar ba.
DUBA WANNAN: Zargin wawurar biliyan N40: Dikko Indi, tsohon shugaban kwastan ya magantu
Saidai hukumar 'yan sanda tayi nasarar cafke matasan biyar kuma ta saki sunayen su da kananan hukumomin da suka fito.
1. Peter Mabiaku - Karamar hukumar Warri ta Arewa
2. Peter Orede - Karamar hukumar Warri ta Kudu
3. Blessing Edjeke - karamar hukumar Ethiope ta Gabas
4. Lucky Okomu - Karamar hukumar Ethiope ta Yamma
5. Prince Enayemo - Karamar hukumar Ughelli ta Kudu
Dukkan mutanen sun fito ne daga jihar Delta.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng