Zargin wawurar biliyan N40: Dikko Indi, tsohon shugaban kwastan ya magantu

Zargin wawurar biliyan N40: Dikko Indi, tsohon shugaban kwastan ya magantu

- Tsohon shugaban hukumar kwastam, Abdullahi Dikko Indi, y ace ya bautawa Najeriya tukuru ba tare da fifita bukatar kan sa ba

- Wata kungiyar ma’aikatan kwastam (COCCO) t ace tsohon shugaban na su ya bawa Najeriya gudunmawa kafin ya yi murabusa a kashin kansa a shekarar 2015

- Hukumar Kwastam ta mika dalar Amurka $375,000 da ta kama a wurin wani dan kasuwa dake kokarin ficewa kasar waje da kudin

Tsohon shugaban hukumar Kwastam, Abdullahi Dikko Indi, y ace batun zayyana sunan sa cikin wadan da suka wawure kudin gwamnati lokacin mulkin PDP ba daidai ba ne tare da musanta ikirarin ministan yada labarai da al’adu, Lai Mohammed, na cewar ana tuhumar sad a almundahanar kudi, biliyan N40bn.

Zargin wawurar biliyan N40: Dikko Indi, tsohon shugaban kwastan ya magantu

Abdullahi Dikko Indi

Dikko na wadannan kalamai ne tab akin wata sanarwa da kungiyar ma’aikatan kwasatam (COCCO) ta fitar a yau kuma ta raba ga kafafen yada labarai, kamar yadda jaridar The Nation ta wallafa.

A cewar kungiyar, Dikko, ya bautawa Najeriya bisa gaskiya da rikon amana kafin daga bisani ya yi murabus bisa kashin kan sa.

DUBA WANNAN: Hukumar 'yan sanda ta gargadi mawakan gayu, ta basu wata shawara

Kungiyar ta kara da cewar, Dikko, ya kawo tsare-tsare a hukumar kwastam musamman a bangaren inganta hanyoyin karbar haraji da yanzu gwamnati ke tutiya da ita.

A yau ne hukumar kwastam ta mikawa hukumar EFCC dalar Amurka $375,000 da ta kama a wurin wani dan kasuwa da yake kokarin fita kasar waje a ranar Asabar, 3 ga watan Maris, a jihar Kaduna.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel