Ana tuhumar wata mai gidan haya da laifin yiwa 'yan hayarta sata

Ana tuhumar wata mai gidan haya da laifin yiwa 'yan hayarta sata

A gurfanar da wata mace mai gidan haya mai shekaru 53, Rita Olukanmi, a kotun Majistare da ke Ikeja inda ake tuhumar ta da zatan kaya wanda darajarsu ya kai N1.4m daga dakin wanda suke haya a gidanta.

Dan sanda mai shigar da kara, Inspecta Victor Eruada ya shaidawa kotu cewa wadda ake tuhumar ta aikata laifin ne tare da wasu mutane a ranar 7 ga watan Janairun 2018 a gida mai lamba 19 layin Oduduwa St. Aboru a jihar Legas.

Yanzu-Yanzu: Majalisa ta bukaci Sifeta Janar na 'Yan sanda ya tabbatar an dawo da sandan majalisar cikin sa'o'i 24
Yanzu-Yanzu: Majalisa ta bukaci Sifeta Janar na 'Yan sanda ya tabbatar an dawo da sandan majalisar cikin sa'o'i 24

Ya cigaba da cewa wanda ake tuhumar, ta shiga gidan Mr. Richard Jacob inda ta sace na'urar dumama abinci (microwave), fanka, tulun gas na girki, na'urar gasa burodi da kuma na'urar decoder na kallon talabijin kirar Gotv.

DUBA WANNAN: Kungiyoyi masu goyon bayan Atiku sunyi barazanar juya masa baya

Ta kuma dauke akwatin kayayaki, dan kune da sarkan zinari, babban firinji, katon din kifi, koton din giya da, na'urar kara magana da faifan bidiyon aurensu da wasu takardu masu muhimmanci wanda kudinsu ya tasanma N1.4m.

Bayan Jacob ya gano kayayakin a dakin mai gidan hayan ne ya kai kara ofishin yan sanda inda aka kama ta kuma aka gurfnar da ita gaban kotu. Laifukan da ta aikata sun sabawa sashi na 411, 287 da 307 na dokar masu laifi na jihar Legas na 2015.

Ana tuhumarta da laifin hadin baki, shiga gida ba izini da kuma sata. Sai dai ta musanta aikata laifukan da aka karanto mata.

Alkalin kotun, Mrs Dan Oni, ta bayar da belin wanda ake tuhuma kan kudi N250,000 da kuma mutane biyu wanda suka tsaya mata. Ta kuma daga sauraron karar zuwa ranar 7 ga watan Mayu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164