Da duminsa: Wasu 'yan majalisar wakilai biyu sun sallama jam'iyyar PDP, sun canja sheka
Wasu 'yan majalisar wakilai guda biyu, a yau, sun bayyana ficewar su daga jam'iyyar PDP yayin zamar majalisar na yau.
A wasikun da 'yan majalisar wakilan suka aike kuma shugaban majalisar, Yakubu Dogara, ya karanta sun bayyana cewar sun canja sheka daga PDP zuwa jam'iyyar APGA.
'Yan majalisar biyu; Ben Nwakwo da Anayo Nnebe, sun bayyana cewar sun fita daga jam'iyyar ta PDP ne saboda rikicin shugabanci da jam'iyyar ke fama da shi a jihar su ta Anambra.
Jaridar premium times ta taba wallafa rahoton cewar dan majalisa Ben Nwakwo ya marawa jam'iyyar APGA baya ne a zaben gwamna da aka yi a jihar a 2017.
Wannnan shine karo na farko da wani mamba a majalisar ta wakilai ya canja sheka zuwa jam'iyyar APGA tunda aka rantsar da majalisar bayan zaben 2015.
DUBA WANNAN: An zo wurin: Matasa sun tafka rikicin siyasa a jihar Bauchi, an rasa rayuka
Ya zuwa yanzu jam'iyyar PDP ta rasa mambobi 15 a majalisar wakilai daga 2015 zuwa yanzu.
Jam'iyyar APGA na da mambobi guda uku, hakan ya saka ta cikin jerin jam'iyyun Najeriya uku dake da wakilci a majalisar wakilai.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng