An zo wurin: Matasa sun tafka rikicin siyasa a jihar Bauchi, an rasa rayuka
- An tabbatar da mutuwar wasu matasa biyu a unguwanni daban-daban dake cikin garin Bauchi
- Matasan sun rasa rayukan su ne a unguwannin Jahun da titin Wanka a garin Bauchi sakamakon rikici a kan lika fostar zabe
- Mazauna titin Wanka sun ce an kashe wani matashi a kofar gidansu kuma tuni har an binne shi bisa tsarin addinin Islama
An tabbatar da mutuwar wasu matasa biyu a unguwanni daban-daban dake cikin garin Bauchi.
Matasan sun rasa rayukan su ne a unguwannin Jahun da titin Wanka a garin Bauchi sakamakon rikici a kan lika fostar zabe.
Mazauna titin Wanka sun ce an kashe wani matashi a kofar gidansu kuma tuni har an binne shi bisa tsarin addinin Islama.

Wani shaidar gani da ido, Mohammed Adam, ya shaidawa jaridar Daily Post cewar an kashe matasan ne a kan rikicin lika fostar zabe ko kuma cire ta.
Kakakin hukumar 'yan sanda a jihar Bauchi, DSP Datti Kamal, ya tabbatar da afkuwar lamarin ga Daily Post.
DUBA WANNAN: Jirgin yakin hukumar soji MI-35M ya yi ruwan nakiyoyi a kan motocin 'yan Boko Haram
A cewar sa, "mun samu rahoton kisan wani matashi, Abdulhaxiz Yunusa, da wasu matasa da ba a san ko su waye ba suka aikata a kofar gidansa."
Ya kara da cewar hukumar 'yan sanda na gudanar da bincike domin gano wadanda keda hannu cikin kisan.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng