An gano gawarwakin 'yan sanda 6 da aka kashe jiya a Benuwe

An gano gawarwakin 'yan sanda 6 da aka kashe jiya a Benuwe

- An gano gawarwakin jami'an y'an sanda guda shida, da aka kashe su ranar lahadi da yamma a jihar Benuwe

- Kakakin hukumar 'yan sandan jihar Benuwe, ASP Moses Yamu, ya ce al'amarin ya faru ne a yankin Anyibe, cikin karamar hukumar Logo dake jihar

- Yamu ya ce, maharan sun farwa y'an sandan ne a tsakanin karfe shida na yammacin jiya Lahadi zuwa wayewar safiyar Litinin

An gano gawarwakin jami'an y'an sanda guda shida, da aka kashe su ranar lahadi da yamma a harin kwanton bauna da ake zargin makiyaya ne suka kai kan jami'an a jihar Benue.

An gano gawarwakin 'yan sanda 6 da aka kashe jiya a Benuwe
Motar 'yan sandan da aka kaiwa hari

Cikin bayanin da hukumar y'an sanda jahar Benue ta sanar, ta bakin jami'in hulda da jama'a ASP Moses Yamu ya ce, al'amarin ya faru ne a yankin Anyibe, cikin karamar hukumar Logo dake jahar ta Benue.

DUBA WANNAN: Kididdigar ta'adin gobara a Legas: Rayuka da biliyoyin da aka yi asara

Yamu ya ce, maharan sun farwa y'an sandan ne a tsakanin karfe shida na yammacin jiya Lahadi zuwa wayewar safiyar Litinin.

Yankin na Logo da Gulma dai na fama da hare-haren da ake zargin makiyaya ne ke yin sa tun farkon wannan shekarar, lamarin da ya yi sanadiyyar salwantar rayukan jama'a da dama.

An gano gawarwakin 'yan sanda 6 da aka kashe jiya a Benuwe
Wurin da aka kaiwa 'yan sandan hari

Ba zamu iya saka karin wasu hotunan gawarwakin 'yan sandan da aka kashe din ba saboda wasu dalilai.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng