Adadin kudin da Buhari ya kashe wajen duba lafiyarsa: Babbar Kotun tarayya ta sanar da ranar yanke hukunci
Mai shari’a John Tsoho na babbar Kotun tarayya dake garin Abuja ya sanar da ranar 5 ga wata Yuni don yanke hukunci game da karar da wasu suka shigar don tilasat ma gwamnati bayyana nawa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kashe a kasar Birtaniya wajen duba lafiyarsa.
Legit.ng ta ruwaito wata kungiya mai rajin kare hakkin bil adama mai suna ASRADI ce ta shigar da kara gwamnan babban bankin Najeriya, Godwin Emefiele kan ya bayyana adadin kudaden da Buhari ya kashe wajen duba lafiyarsa.
KU KARANTA: Idan ka ji Dattijon banza, Yaron banza ne: Yadda wani Dattijon biri ke biyan kananan yara N100 yana kwanciya dasu
Hakazalika, kungiyar ASRADI ta hannun shugabanta Adeolu Oyinlola ta nemi ta ji nawa gwamnati ta kashe wajen daukar dawainiyar tawagar shugaban kasa, da kuma jirginsa na tsawon kwaani 103 da suka kwashe a Landan.
Bugu da kari, ASRADI ta bukaci babban banki ta biyata diyyar naira miliyan 10 saboda kin amincewa ta baya wadannan bayanai kamar yadda ta bukata, duk da kuwa kundin tsarin mulki yayi wannan tanadi.
Sai dai a zaman sauraron karar na 16 ga watan Feburairu, lauyoyin babban bankin Najeriya sun yi watsi da wannan bukata ta ASRADI, inda tace baya cikin huruminta ta bayyana wadannan bayanai, inda ta buakci Kotu tayi watsi da karar gabaki daya.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng