Zaben fidda gwani na takarar kujerar shugaban kasa: Idan muka kwaikwayi PDP sunanmu fadɗadɗu – Buba Galadima

Zaben fidda gwani na takarar kujerar shugaban kasa: Idan muka kwaikwayi PDP sunanmu fadɗadɗu – Buba Galadima

Jigo a jam’iyyar APC, kuma tsohon aminin shugaban kasa Muhammadu Buhari, Alhaji Buba Galadima yayi wata kashedi ga jam’iyyar APC na cewa kada ta kuskura ta tafka irin kuren da PDP ta tafka game da fidda dan takara a zaben 2019.

Buba ya bayyana haka ne cikin wata hira da yayi da gidan rediyon BBC Hausa, inda yace muddin APC ta kwaikwayi jam’iyyar PDP wajen yin dauki daura a game da fidda dan takarar shugaban kasa, tabbas sunansu fadaddu.

KU KARANTA: Ga koshi ga kwanar yunwa: An hallaka wani matashi bayan ya ciyo naira miliyan 11 a caca

“Tun daga shekarar 1999 sai anyi gumurzu a jam’iyyar PDP kafin a fidda dan takara, kuma suna cin zabe, har sai shekarar 2015 da suka yi ma Jonathan dauki daura, kuma ya fadi zabe.

“Amma Buhari bai taba cin zaben cikin gida ba, bashi takara ake yi, kuma bai taba cin zabe ba, har sai a shekarar 2015 da ya kada sauran yan takarkaru a zaben fidda gwani. Don haka matuka muka yi koyi da PDP a zaben 2019, tabbas sunanmu fadaddu.” Ini shi

Dama dai tun a gabanin zabukan 2015 ne Dangantaka ta yi tsami tsakanin shugaban kasa Muhammadu Buhari da Buba Galadima, wanda hakan yayi sanadin Buba yaki goya ma Buhari baya a zaben 2015, inda ya bi bayan Kwankwaso.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng