Bukola Saraki ya biya Masu Unguwanni albashin su da ya makale na tsawon lokaci
- Bukola Saraki ya dauko nauyin biyan masu gari albashin su da ya ki fitowa
- Tsohon Gwamnan na Jihar Kwara ya cire kusan Miliyan 50 daga aljihun sa
- Sarakunan da su ka tagayyara sun dai yabawa Shugaban Majalisar Dattawan
Turakin Ilorin watau Bukola Saraki ya biya Sarakunan Kasar Kwara wasu albashin su da su ka makale na wata da watanni wanda har wasu sun fara cire ran cewa kudin za su fito. Alangua na Ibagun, Alhaji Jimoh Alabi yace sun ji dadin hakan.
Shugaban Majalisar Dattawan yayi wa Sarakunan Yankin da ya fito ruwan bashin albashin su da aka yi watanni 20 ba a biya su ba. Ko da dai hakkin ya rataya ne a kan Kananan Hukumomi, Shugaban Majalisar ya biya kudin da kan sa.
KU KARANTA: Yadda rikicin Limanci ya kawo rigima a babban Masallacin Kaduna
Sarakunan Yankin Asa da Kananan Hukumomin Ilorin da Gabas da Kudu sun ji maiko bayan da Saraki ya biya su albashin su da su ke bi bashi. Abin da tsohon Gwamnan ya cire daga aljihun sa ya haura Naira Miliyan 49 inji wani Hadimin sa.
Hakimai da Dagatai da masu Unguwanni 220 ne aka dauki sama da shekara guda da rabi ba a biya su albashin su ba. Dalilin haka ne Sanata Bukola Saraki yayi bincike game da lamarin ya kawo masu dauki domin su sauke nauyin da ke wuyan su.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng