Tsohon dan Firamare yayi shekara hudu yana yiwa aikin Likitanci sojan gona

Tsohon dan Firamare yayi shekara hudu yana yiwa aikin Likitanci sojan gona

- Hukumar ‘Yan Sanda a jihar Legas ta kama wani Abdulrahman Mohammed da laifin yiwa aikin likitanci sojan gona

- Mohammed makarantar Firamare kadai y agama, amma yayi shekaru hudu yana sojan gona a aikin likitanci kafin a kamashi

- An kamashi da magunguna da abun awon zuciya da allurai da abun awon hawan jinni da Karin ruwa da sauran kayayyakin da ake duba mara lafiya dasu

Hukumar ‘Yan Sanda a jihar Legas ta kama wani Abdulrahman Mohammed da laifin yiwa aikin likitanci sojan gona.

Mohammed makarantar Firamare kadai ya gama, amma yayi shekaru hudu yana sojan gona a aikin likitanci kafin a kama shi a ranar Asabar.

Tsohon dan Firamare yayi shekara hudu yana yiwa aikin Likitanci sojan gona

Tsohon dan Firamare yayi shekara hudu yana yiwa aikin Likitanci sojan gona

An kamashi da magunguna da abun awon zuciya da allurai da abun awon hawan jini da karin ruwa da sauran kayayyakin da ake duba mara lafiya dasu, a shagonsa dake Bamishile, Idi-Araba inda yake duba marasa lafiya.

KU KARANTA KUMA: Yadda Jama’a su ka tarbi tsohon Gwamnan Kano a Garin Shugaban kasa

Kwamishinan ‘Yan Sandan Edgal Imohimi, a ranar Litinin, mutumin mai shekaru 39, wanda ya fito daga kauyen Ran dake karamar hukumar Ngala a jihar Borno, har allura yake yiwa mutane kafin ranar 14 ga watan Afirilu lokacin da jami’an ‘Yan Sanda suka kamashi.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel