An tsinci fiye da miliyan biyu a wurin hatsarin mota da ya kashe mutane 5 a Bauchi
- Wani hatsarin mota ya hallaka mutane biyar tare da jikkata wasu mutane tara a jihar Bauchi.
- Kwamandan hukumar kiyaye hadurra shiyyar Azare a jihar Bauchi, Sama'ila Shehu, ya bayyana cewar hatsarin ya afku ne ranar Asabar a kan titin Azare zuwa Potiskum
- An garzaya da fasinjojin da suka samu raunuka zuwa cibiyar kula da lafiya ta tarayya dake Azare yayin da aka tabbatar da mutuwar mutane biyar
Wani hatsarin mota ya hallaka mutane biyar tare da jikkata wasu mutane tara a jihar Bauchi.
Kwamandan hukumar kiyaye hadurra shiyyar Azare a jihar Bauchi, Sama'ila Shehu, ya bayyana cewar hatsarin ya afku ne ranar Asabar a kan titin Azare zuwa Potiskum.
A cewar kwamandan, hatsari ya faru ne bayan tayar wata babbar mota ta fashe a dai-dai kauyen Buskuri mai nisan kilomita 15 daga Azare.
Bayan fashewar tayar babbar motar ne, sai direban ya kasa sarrafa ta har ta je ta daki wata motar fasinjoji kirar Sharon mai lamba KRS 25 XA dake tafiya zuwa Potiskum daga jihar Sokoto.
Shehu ya kara da cewa, suna samun rahoton abinda ya faru suka tura jami'an su domin ceton rayukan jama'ar da hatsarin ya ritsa da su.
DUBA WANNAN: 'Yan Boko Haram sun sanni kuma suna tsoro na don ina kama su ko na kashe su - Aisha mafarauciya
An garzaya da fasinjojin da suka samu raunuka zuwa cibiyar kula da lafiya ta tarayya dake Azare yayin da aka ajiye kayayyakin su a ofishin hukumar kiyaye hadurra.
An tabbatar da mutuwar mutane biyar daga cikin wadanda hatsarin ya ritsa da su.
Kazalika, an samu kudi da yawansu ya kai miliyan N2,133,075 kuma tuni an damka su hannun dangin masu kudin a gaban jami'an hukumar 'yan sanda.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng