Jerin shararrun matan da aka fi kauna a kaf Duniya

Jerin shararrun matan da aka fi kauna a kaf Duniya

Kwanaki mun kawo maku jerin mutanen da su ka fi farin jini a Duniya inda ku ka ji sunaye irin su Bill Gates, Cristiano Ronaldo, da Barrack Obama. Wannan karo kuma mun kawo maku jerin matan da su ka fi kowa baiwar farin jini ne.

YouGov ce tayi nazari inda ta bayyana sanannun matan da su ka fi shahara a Duniya daga ciki akwai manyan Mawaka da masu mulki da ma ‘Yan mata. Sai dai a cikin jerin babu 'Yar Najeriya ko ma Afrika ko da mutum guda.

Jerin shararrun matan da aka fi kauna a kaf Duniya

Matar Obama na cikin matan da su ka fi yawan masoya

1. Angelina Jolie

Ta farko a jerin ita ce Angelina Jolie wanda ta rabu da Mijin ta watau Brad Pitt kwanakin baya. Yanzu haka Jolie tana fama da cutar kansa.

2. Michelle Obama

Duk Duniya dai babu gidan da su ka tara masoya a Duniya irin Gidan Barrack Obama. Ban da farin jinin sa, matar sa ma tana da masoya.

KU KARANTA:

3. Oprah Winfrey

Oprah fitacciyar ‘yar kasuwa ce kuma babbar ‘Yar jarida a Amurka. Oprah ko da ba ta taba aure ba, tana da dinbin masu kaunar ta a Duniya.

4. Queen Elizabeth

Sarauniyar Ingila, Elizabeth tana da tarin Masoya wanda ta zo ta 4 a jerin da YouGov ta fitar. Elizabeth II ta dade a kan sarautar Ingila.

5. Hillary Clinton

Tsohuwar Sakatariyar Gwamnatin Amurka kuma ‘Yar takarar Shugabar kasar a zaben 2016 Clinton tana da masu kaunar ta kwarai da gaske a Duniya.

Sauran masu farin jini a Duniyar sun hada da Emma Watson, Malala Yousafzai da Shugabar Jamus Angela Merkel da kuma Mawakan nan Taylor Swift da kuma Madonna.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel