IBB ya mayar da martani a kan zawarcin da jam'iyyar SDP ke yi masa

IBB ya mayar da martani a kan zawarcin da jam'iyyar SDP ke yi masa

- Tsohon shugaban kasar nan na mulkin soja, janar Ibrahim Badamasi Babangida, ya ce ya yi tsufa da shiga jam'iyyar siyasa

- IBB na wannan kalami ne yayin da yake karbar bakuncin shugabannin jam'iyyar karkashin jagorancin shugabanta, Olu Falae wanda shine sakataren Tsohon shugaban kasar a zamanin mulkinsa

- Dattaijan arewa sun kaiwa IBB wata ziyara a jiya a gidansa dake kan wani tsauni a garin Minna dake jihar Neja

Tsohon shugaban kasar nan na mulkin soja, Janar Ibrahim Badamasi Babangida, da ake yiwa lakabi da "Maradona a siyasa" ya bayyanawa shakkun hadewarsa da sabuwar jam'iyyar SDP sakamakon tsufan da ya ce ya riske shi.

Babangida ya ce: "Ba don tsufa ya cimma ni ba, ko shakka babu zan so hadewa da jam'iyyar nan taku. Nayi imani kan manufar jam'iyyar ku da abinda take a kai."

IBB ya mayar da martani a kan zawarcin da jam'iyyar SDP ke yi masa

IBB ya mayar da martani a kan zawarcin da jam'iyyar SDP ke yi masa

Sai dai kuma, yayin da yake karbar bakuncin shugabannin jam'iyyar karkashin jagorancin shugabanta, Olu Falae wanda shine sakataren Tsohon shugaban kasar a zamanin mulkinsa, janar Ibrahim Badamasi ya nuna goyon bayan sa ga sabuwar jam'iyyar da cewa ita ce zabin da ya ragewa y'an Nigeria daga mulkin youjam'iyyun PDP da APC.

DUBA WANNAN: IBB ya mika kokon bara ga 'yan Najeriya dangane da zaben 2019

Bayan rubuta doguwa wasika ga shugaba Buhari tare da bashi shawarar ya hakura da tsayawa takara a 2019, tsohon shugaban kasar Najeriya a mulkin soji, Janar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB) ya bukaci 'yan Najeriya da su kada kuri'un su ga matasa kawai a zaben 2019.

Legit.ng ta rawaito cewar IBB na wadannan kalamai ne a gidansa dake Minna dake jihar Neja yayin da ya karbi bakuncin wata kungiyar matasa "YES Nigeria Movement".

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Mailfire view pixel