Uwargida ta shiryawa mijinta da sabuwar amaryar sa liyafa, kalli hotuna

Uwargida ta shiryawa mijinta da sabuwar amaryar sa liyafa, kalli hotuna

- sabanin abinda aka saba gani ko ji mata na yi idan za a yi masu kishiya, wata mata ta nuna halin dattako da yakana ga mijinta

- Ta nunawa mijinta halacci ta hanyar shirya masa liyafa bayan ya yi mata kishiya

- A wurin liyafar, uwargidan ta bawa amarya abinci a baki cikin farin ciki da sakin fuska

Halin wata uwargida na dattako, yakana da nuna halacci ga mijinta ya jawo hankalin jama'ar Najeriya, musamman a dandalin sada zumunta.

Matar ta nuna juriya da jarumta ta hanyar shiryawa mijinta liyafa domin taya shi murnar kara aure da kuma yiwa abokiyar zamanta (amarya) murnar shigowa cikin gidansu.

Uwargida ta shiryawa mijinta da sabuwar amaryar sa liyafa, kalli hotuna
Uwargida ta shiryawa mijinta da sabuwar amaryar sa liyafa

Hatta mijin da sabuwar amaryar sa, sun yi matukar mamakin wannan abu da uwargidan tayi.

DUBA WANNAN: Fallasa: An tafka magudi a zaben 2015 a arewa - Dattijo Tanko Yakasai

Hotunan taron liyafar sun samu tagomashi a dandalin sada zumunta inda jama'a ke cigaba da bayyana ra'ayin su.

A wurin taron liyafar, an ga uwargidan na bawa kishiyar ta, wato amarya, abinci a baki.

Uwargidan ta sha yabo wurin jama'a, har wasu na kiranta 'yar aljanna tare da fatan samu yawaitar masu irin halayyar ta cikin mata.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng