Maulidin Sheikh Nyass: Ina yi wa yan Tijjanawa bangajiya - Sanata Kwankwaso

Maulidin Sheikh Nyass: Ina yi wa yan Tijjanawa bangajiya - Sanata Kwankwaso

Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya aika sakon ban gajiya ga miliyoyin mabiya darikar Tijjaniya da suka halarci gagarumin taron Maulidin Shehun Ibrahim wanda aka gudanar babban birnin tarayya da jihar Kaduna a ranar Asabar, 14 ga watan Afrilu.

Kwankwaso wanda ya kasance daya daga cikin manyan masu ruwa da tsakin da suka halarci taron, ya nuna farin cikinsa ga yadda aka gudanar da taron cikin aminci ba tare da an samu ko wacce Baraka ba duk da yawan mutanen da suka hallara.

Maulidin Sheikh Nyass: Ina yi wa yan Tijjanawa bangajiya - Sanata Kwankwaso
Maulidin Sheikh Nyass: Ina yi wa yan Tijjanawa bangajiya - Sanata Kwankwaso

Zuwan na Sanata Kwankwaso wurin Mauludin ya yi matukar daukar hankalin mahalarta taron, inda dimbin jama'a suka mamaye motarsa tamkar za su hadiye shi da tawagarsa.

KU KARANTA KUMA: Dandazon jama’a sun taru bayan hoton Shehu Inyass ya bayyana a maulidin Abuja

Sanatan ya bayyana hakan ne ta bakin hadiminsa Shehu M. Bello (Shehun Garu) wanda shine Jagoran Kwankwasiyya Na Jihar Jigawa. Inda kuma ya yi fatan Allah ya mayar da kowa gidansa lafiya kamar yadda aka zo lafiya.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng