Wata budurwa ta hallaka mahaifinta saboda yana adawa da saurayinta
Hukumar 'yan sandan Najeriya reshen jihar Abuja ta cika hannu da wata yarinya, Emani Kure; mai shekaru 16 bisa kashe mahaifinta, Kusha Kure; mai shekaru 40.
Emani ta kashe mahaifinta, Kusha, saboda ya ki yarda da saurayinta, Nasiru Musa, ya aure ta a matsayin mace ta biyu.
Jaridar Sun ta rawaito cewar, Emani da Musa, sun shafe fiye da shekaru biyu suna soyayya duk da mahaifinta baya son soyayyar ta su.
Emani ta yanke shawarar kashe mahaifin nata ne saboda ya yi watsi da bukatar Nasiru na son ya aure ta.
Emani da iyayenta na zaune a kauyen Karavan dake karamar hukumar Bwari dake Abuja kuma tuni ta amsa laifinta yayin fuskantar tuhuma a hannun 'yan sanda.
DUBA WANNAN: Shugaba Buhari ya bayyana mutanen da suka jefa 'ya Najeriya cikin fatara da talauci
Mahaifiyar budurwar, Asabe; mai shekaru 35, ta musanta cewar da hadin bakinta aka kashe mijin nata tare da bayyana cewar dukkansu basa goyon bayan soyayyar Emani da Nasiru.
Emani, mahaifiyar ta, da saurayinta na tsare a ofishin hukumar 'yan sanda inda ake cigaba da bincike a kansu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng