Dandazon jama’a sun taru bayan hoton Shehu Inyass ya bayyana a maulidin Abuja
Rahotanni daga babban birnin tarayya Abuja sun nuna cewa Sheikh Ibrahim Inyass ya bayyana a jikin fitilar haska titi dake wajen taron Maulidi.
Bayyanar sa ke da wuya daruruwan mabiya darikar Tijjaniya sukayi da'ira suna zikiri tare da dubiya domin ganin shi.
An samu wani hazikin matashi masoyin manzon Allah da ya hau kololuwar fitilar ya kuma sumbaci wajen da shehin ya bayyana.
A ranar dai Asabar 14 ga watan Afrilu ne aka gudanar da gagarumin taron Maulidin Shehun wanda sheikh Dahiru Bauchi ya jagoranta.
KU KARANTA KUMA: Kowa ma ya sani wallahi miliyan 50 Atiku ya bani – Fati Mohammed ga magoya bayan Buhari
Daga cikin wadanda suka halarci taron akwai manyan yan siyasa kamar su Kwankwaso da Shehu Sani.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng