Dandalin Kannywood: 'Yan sanda sun cika hannuwan su da 'yan fim 28 suna 'shutin' a Zariya

Dandalin Kannywood: 'Yan sanda sun cika hannuwan su da 'yan fim 28 suna 'shutin' a Zariya

- 'Yan sanda sun cika hannuwan su da 'yan fim 28 a Kaduna

- Mun samu labarin hakan daga majiyar mu ta mujallar FIM

- 'Yan sandan sun ce sun kama su ne a bisa zargin cewa su wai ‘yan Shi’a

Kamar dai yadda muka samu daga majiyar mu FIM, daya daga cikin fitattun daraktocin masana'antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood watau Kabiru S. Yaro wanda aka fi sani da Kokobi tare da wasu mutane ashirin da bakwai ne suka shiga hannun ‘yan sanda a garin Zariya, Jihar Kaduna.

Dandalin Kannywood: 'Yan sanda sun cika hannuwan su da 'yan fim 28 suna 'shutin' a Zariya

Dandalin Kannywood: 'Yan sanda sun cika hannuwan su da 'yan fim 28 suna 'shutin' a Zariya

KU KARANTA: An kafa kwamitin mutum 28 don tsaftace harkar fim

Kamar yadda muka samu kuma, yan sandan sun ce sun kama su ne a bisa zargin cewa su wai ‘yan Shi’a ne kuma suna kokarin tada zaune-tsaye.

Legit.ng ta samu haka zalika cewa wannan lamarin dai ya faru ne a ranar Litinin din da ta gabata , 9 ga Afrilu, 2018 a yayin da su 'yan fim din su ke shirin daukar wani fim.

haka ma dai mun samu cewa wadannan 'yan fim din sai da suka kwana a ofishin 'yan sanda a garin Zariya sannan kuma har kotu aka kai su inda aka ci su tara kafin a bayar da belin su.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel