Barkewar sabon rikicin kabilanci a jihar Kogi: An kashe mutane 5, an kona gidaje 50
A kalla mutane biyar ne rahotanni suka bayyana mutuwar su a wani sabon rikicin kabilanci da ya barke tsakanin kabilun Igala da Bassa Kwomu dake jihar Kogi.
Kazalika an kona gidaje fiye da 50 a garin Aloko-Oguma dake karkashin karamar hukumar Bassa a jihar.
Rahotanni sun ce rikici ya barke tsakanin kabilar Bassa Kwomu da Igala a kan ikon noman kashu har ta kai ga 'yan kabilar Bassa Kwomu sun kashe wani Igala kuma sun binne shi a asirce.
Saidai bayan gano kabarin da aka binne dan uwansu, 'yan kabilar Igala sun kai farmaki kan 'yan Bassa Kwomu tare da kashe mutane biyar da kuma kona gidaje fiye da 50.
DUBA WANNAN: Sheikh El-Zakzaky: Magoya bayan Shi'a sun mamaye manyan titunan Abuja
Wata majiya ta shaida mana cewar an dade ana takun saka tsakanin kabilun biyu tare da bayyana cewar dama dukkan kabilun na neman hanyar kaiwa juna hari.
Kakakin hukumar 'yan sanda a jihar Kogi, ASP William Aya, ya tabbatar da faruwar lamarin, saidai ya karyata batun mutuwar mutane biyar tare da bayyana cewar mutum daya ne kawai ya mutu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng