Sheikh El-Zakzaky: Magoya bayan Shi'a sun mamaye manyan titunan Abuja

Sheikh El-Zakzaky: Magoya bayan Shi'a sun mamaye manyan titunan Abuja

A jiya Asabar ne magoya bayan darikar Shi'a suka mamaye manyan tituna a garin Abuja a wata sabuwar zanga-zangar neman sakin shugaban su Sheikh Ibrahim El-Zakzaky, da gwamnati ke tsare da shi tun shekarar 2015.

Tun shekarar 2017 magoya bayan Shi'a ke gudanar da zanga-zanga a Abuja ta hanyar yin zaman dirshan a Unity Fountain domin tursasa gwamnati sakin shugaban su.

Saidai a zanga-zangar ta jiya, magoya bayan Shi'a sun mamaye hanyoyin da zasu sada mutane da zauren majalisar kasa.

Sheikh El-Zakzaky: Magoya bayan Shi'a sun mamaye manyan titunan Abuja
Sheikh El-Zakzaky

Ko a keanaki biyu da suka gabata saida magoya bayan Shi'ar suka mamaye mashigar babban filin wasa na Abuja, inda suka tafi da kayan girki domin yin shirin zaman dirshan, saidai jami'an tsaro sun hana su shiga cikin filin wasan.

Zanga-zangar ta dauki sabon salo a jiya a yayin da dubban 'yan Shi'a suka fito tare da mamaye manyan titunan Abuja, lamarin da ya haddasa cunkuson ababen hawa.

DUBA WANNAN: Aisha Buhari ta sake yin magana a kan goyawa mijinta baya a 2019

Rahotanni sun bayyana cewar hatta jami'an 'yan sanda da aka turo domin dakatar da zanga-zangar, 'yan Shi'ar sun gagare su.

Kokarin jin ta bakin kakakin hukumar 'yan sanda na Abuja bai samu ba, saboda bai amsa duk kiran da jaridar Today.ng ta ce tayi masa ba.

Har lokacin rubuta wannan labarin, magoya bayan Shi'ar na cigaba da barkowa daga wurare daban-daban tare da kara mamaye cikin kwaryar birnin garin Abuja.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng