Jerin ‘Yan matan da su ka zarce kowa kyau a Kasar nan

Jerin ‘Yan matan da su ka zarce kowa kyau a Kasar nan

Idan ba ku manta ba a baya mun kawo maku jerin sanannun mutanen da su ka fi kowa yawan a Duniya. Wannan karo kuma mun shiga fannin ‘Yan mata ne inda mu ka kawo maku wadanda su ka fi kowa kyau a Najeriya.

Ga dai wadanda ake tunanin cewa babu kamar su duk fadin kasar:

Jerin ‘Yan matan da su ka zarce kowa kyau a Kasar nan
Geneveive na cikin ‘Yan matan da ba su da sa'a wajen kyau

1. Genevieve Nnaji

Da dama an yi ittifaki babu wanda ta kai Genevive kyau a Najeriya. An haifi shararriyar ‘Yar wasan kwaikwayon ne a Garin Mbiase a cikin Jihar Imo kusan shekaru 40 da su ka wuce.

KU KARANTA: Mutane 10 da su ka fi kowa farin jini a kaf Duniya a 2018

Jerin ‘Yan matan da su ka zarce kowa kyau a Kasar nan
Agbani Agbero tayi fice a Duniya ba ma Najeriya ba

2. Agbani Darego

Agbai Darego wata ‘Yar kwalisa ce asalin ‘Yar Jihar Ribas. Ta taba karbar lambar yabo a matsayin wanda ta fi kowa kyau a Najeriya har ma da Afrika a 2001. Darego tana cikin kyawawan matan Duniya.

Jerin ‘Yan matan da su ka zarce kowa kyau a Kasar nan
Oluchi mai shekaru 37 tana cikin kyawawan Najeriya

3. Oluchi Onwaegba

Ana sa Oluchi Onwaegba wanda ta fito daga Kudancin Najeriya cikin kyawawan da ake ji da su a Najeriya. An haifi Oluchi ne a 1980 kuma ta shahara wajen harkar kwalliya da kele-kele.

Bayan wadannan dai akwai irin su Slyvia Nduka wanda ta shahara a Duniya da kuma Adaora Akubilo wata Budurwa ‘Yar asalin Najeriya da ke Amurka.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng