'Yan Shi'a sun raba ruwan gora a maulidin 'yan darika a Abuja
A jiya ne dimbin mabiya darika Tijaniyya a fadin Najeriya sukayi taron Maulidin Sheikh Ibrahim Inyass da aka saba yi duk shekara a wurare daban-daban tun tunawa da ranar haihuwar Shehun Malami Ibrahim Inyass.
Taron Maulidin da aka gudanar a dandalin taro na Eagles Square a Abuja ya sami hallarton manya-manya malamai, ma'aikatun gwamnati, yan kasuwa da yan siyasa ciki har da tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.
A wajen wannan taro ne aka ga mabiya Shi'a suma sun hallarta don taya murnar har suka kawo gudunmawa na ruwan gora wanda ke dauke da takarda mai hotunnan Sheikh Ibrahim Inyass tare da Sheikh Ibrahim El-Zakzaky wanda ya dade yana tsare tun bayan da aka samu rashin jintuwa tsakanin mabiyansa da sojin najeriya a Zaria.
Gudunmawar da yan Shi'a suka kai wajen Maulidin ya janyo cece-kuce dandalin sada zumunta inda wasu suke sanya albarka kan yadda al'umman musulmi ke kara hadewa wuri guda suna kaunan juna duk da banbancin akida yayinda wasu suke ganin kawai anayi ne da wata manufa.
Ga dai hotunan ruwan gorar yayinda wasu samari ke sanya masa takarda mai dauke da hotunan Sheikh Ibrahim Inyass da Sheikh El-Zakzaky.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng