Abin mamaki: Wata mace da aka sace shekaru 28 da suka gabata ta bayyana
- Yan sanda sun gano wata mata wadda aka sace ta shekaru 28 da suka gabata
- Matar tace wani tsoho ne ya sace ta yayinda ta tafi rubuta jarabawar JAMB a garin Calabar kuma yayi amfani da asiri ya tsare ta
- Yan sanda sun tarar da miyagun kwayoyi da bindigogi cike da wata mota a gidan dattijon
Jami'an Yan sanda a jihar Benuwe sun ceto wata mata, Martha Eyong mai shekaru 40 yar asalin kasar Kamaru wadda aka sace tun 1990 a yayin da taje rubuta jarabawar shika jami'a wato JAMB a birnin Calabar.
Kamar yadda da shaidawa Channels TV, Ms Eyong tace wani tsohon mai shekaru 78, Ali Omonya Ameh ne ya sace lokacin tana da shekaru 16 kuma ya bada mata wani farin abu mai kama da hoda, kuma tun lokacin tana aikata duk abinda ya umurce ta.
DUBA WANNAN: An kama manyan makamai a jihar Filato, da kuma masu fyade har 24
Ta kuma ce da farko an tafi da ita Legas, daga baya kuma aka dawo da ita karamar hukumar Otukpo na jihar Benuwe inda ta kashe shekaru tana rayuwa cikin kadaici, kunci da barazana har ta kai ga ta haifawa tsohon yara biyu saboda fyade da yake mata.
Yayin da yake magana a kan batun, Mmahaifin matar da aka sace, Michael Eyong, ya bayyana halin bakin cikin daya shiga a dalilin neman diyarsa tun 1990 kuma ya yi kira da hukuma ta bi diyarsa hakkin ta saboda wannan cin zarafin dan adam ne.
Kwamishina Yan sanda na jihar, Fatai Owoseni ya ce wannan abu ne mai matukar ban mamaki inda ya kara da cewa za'a gudanar da sahihiyar bincike kuma a hukunta duk wanda aka samu da laifi.
Kwamishinan ya kuma kara da cewa an gano wata mota cike da kwayoyin tramadol, kayayakin sojoji da kuma bindigogi wanda ake kerawa a Najeriya tare da mutumin da ake zargin.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng