Laifin kisa: An yankewa wani saja hukuncin kisa ta hanyar rataya
- Kotu ta yanke hukuncin kisa ta hanyar rataya a kan wani Dan sanda, Vincent manu, da ya kashe wani dan kasuwa da gangan
- Dan sanda tare da wasu abokan aikinsa guda biyar sun kashe, Stephen Anakwe ne kuma suka birne gawarshi ba tare da sanar da iyalan shi ba
- Dan uwan marigayin ya bayyana godiyarsa ga Ubangiji yadda yayi musu sakayya bayan an kwashe shekaru 6 ana shari'ah
Wata babban kotun da ke zaune a Lafia, babban birnin jihar Nasarawa ta yanke hukuncin kisa a kan wani Saja na 'Yan sanda, Vincent Manu saboda samun shi da hannu wajen kisan wani dan kasuwa, Stephen Anakwe wanda yayi wa sharrin cewa dan fashi da makami ne.
An gurganar da Manu ne tare da wasu Yan sanda guda biyar; Inspecta Danladi Lenkem, Inspector Edula Ateku (wanda ya rasu yayinda ake shari'ar); Kofur Samson Magga, Kofur Musa Audu da kuma Christopher Maikasuwa wanda duk ake tuhumansu da laifin kashe marigayin yayin da suke aikin sintiri.
DUBA WANNAN: Anyi babban kamu: Manyan Boko Haram 8 sunzo hannu
Alkalin kotun, Mai shari'ah James Abundega yace lauya mai shigar da kara ya gamsar da kotu ta hanyar gabatar da shaidu da dalilai cewa da gangan ne aka kashe marigayin wanda hakan laifi ne da yaci karo da sashi 220 na penal code kuma akwai hukuncin daya dace da laifin a sashi na 221.
Alkalin ya wanke sauran Jami'an Yan sandan daga guda biyar inda shi kuma Manu zai fusakanci hukuncin rataya kamar yadda doka ta tanadar wa irin laifin daya aikata.
Dan uwan marigayin mai suna Stephen Anakwe ya bayyana godiyarsa ga Ubangiji bisa hukuncin da aka zartar inda yace bayan shekaru shida ana gudanar da shari'ar, daga karshe an kotu ta bi musu hakkin su.
Lauya mai shigar da kara yace, a daren da yan sandan suka kashe mamacin yayin da suke sintiri, sun tafi wani wurin boyaye ne inda suka birne shi ba tare da sanar da iyalansa ba.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng