Hadimin gwamnan Akwa Ibom ya sauya sheka zuwa jam'iyyar APC

Hadimin gwamnan Akwa Ibom ya sauya sheka zuwa jam'iyyar APC

Mr. Ibanga Etang, hadimin gwamnan jihar Akwa Ibom, Udon Emmanuel ya sauya sheka zuwa jam'iyyar APC. Cikin watannin da suka shude, mai taimakwa gwamnan na musamman a harkokin zabe, Mr. Chris Okorie shima ya canje sheka daga PDP zuwa APC.

Etang wanda tsohon shugaban karamar hukumar Esit Eket ne yayi murabus a ranar 9 ga watan Afrilu a mastayinsa a mai taimakawa gwamnan a fanin kwangiloli sannan ya yi rajista da jam'iyyar APC a mazabarsa ta Etebi tare da wasu magoya bayansa guda 300 a ranar 10 ga watan Afrilu.

Hadimin wani gwamnan PDP ya sauya sheka zuwa jam'iyyar APC
Hadimin wani gwamnan PDP ya sauya sheka zuwa jam'iyyar APC

A yayin da yake jawabi ga magoya bayansa a ranar Juma'a, Etang shigarsu jam'iyyar APC ya karawa jam'iyyar kwarjini kuma yana sa ran jam'iyyar ne zata lashe zabe a karamar hukumar ta Esit Eket.

DUBA WANNAN: An damke wani dan shekaru 22 da laifin yiwa yar shekara 13 fyade

Etang ya bayyana cewa ya baro PDP ne saboda wasu tsiraru a jam'iyyar sunyi babakere kan mulkin kuma basu damawa da kowa. Ya kuma ce dalilin da yasa mutane ke barin jam'iyyar PDP a yankin shine yadda wani mutum tilo yake juya karamar hukumar kamar wani abin daya malaka.

Kamfanin dillanci labarai na kasa (NAN) ta ruwaito cewa Etang yayi aiki a matsayin mataimaki na musamman ga tsohon gwamnan jihar Godswill Akpabio a karkashin jam'iyyar PDP.

A yayin da yake karban sabbin mambobin, tsohon dan majalisar wakilai, Mr. Bassey Dan-Abia Jnr yace yadda mutane da yawa ke tururuwa zuwa jam'iyyar alama ce da ke nuna jam'iyyar zata karbe ragamar mulkin jihar a 2019.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164