Waiwaye akan rayuwar Sheikh Ja'afar Adam yayinda ya cika shekaru 11 da rasuwa a yau
A dai rana mai kamar ta yau ne wato 13 ga watan Afrilu amma a shekarar 2007 Allah ya dauki ran fitaccen malamin addinin Musulunci Sheikh Ja'afar Mahmoud Adam. Malamin ya rasu ne sakamakon harbin bindiga da akayi masa yayin da yake limancin sallar Asuba a wani masallaci a Kano.
Tarihi ba zai manta da fitaccen shaihun malamin ba saboda irin gudunmawa daya bayar ga cigaban ilimi da koma yadda adinin musunlunci a gida Najeriya da ma wasu kasashen Afirka. Duk da cewa malamin ya dade da rasuwa, koyarwarsa daya bari har yanzu suna kara wanzuwa cikin al'umma ta kafafen yadda labarai da sada zumunta a duniya.
A rana irin wannan zai dace a tunatar da mai karanta kan wasu muhimman abubuwa game da rayuwar shaihin malamin.
1) Haihuwarsa
An haifi marigayi Sheikh Ja'afar Adam ne a garin Daura a shekarar 1962 (Ko kuma 1964 kamar yadda ya fadi a wasu lokutan)
2) Karatun Allo da haddar Kur'ani
Marigayin ya fara karatun allo ne wajen mijin yayarsa, Mallam Haruna, daga bisani kuma aka mayar dashi wajen Malam Umaru a wani gari mai suna Koza, kimanin kilomita 9 a arewacin Daura, wanda shi yayi sanadiyar zuwan sa Kano a 1971 inda ya zauna a makarantar Mallam Abdullahi a Unguwar Fagge a Kano. Marigayin ya fara haddar kurani tun yana karami kuma ya kammala a shekarar 1978.
3) Karatun Boko
Marigayin ya kasance mai sha'awar ilimi, hakan yasa ya shiga makarantu biyu a lokaci guda; makarantar koyon larabci ta mutanen Misra Markaz a cibiyar yada Al'adun Misra, (Egyptian Cultural Centre) a Kano da kuma makarantar manya na yaki da jahilci a shekarar 1980 kuma ya kammala a 1983.
Kammala makarantar yaki da jahilcin ke da wuya sai marigayin da shiga makarantar GATC Gwale duk dai a Kano a shekarar 1984 kuma ya kammala a 1988.
4) Karatun Jami'a
Sheikh Ja'afar ya sami gurbin karatu a Jami'ar musulunci na Madina a kasar Saudiyya inda ya karanci Ilimin Tafsiri daga shekarar 1989 zuwa 1993.
Malamin kuma ya yi nasarar kammala digirinsa na biyu (Masters) a Jami'ar Kasa-da-Kasa ta Afirka da ke birnin Khartoum a kasar Sudan.
Kafin rasuwarsa, Shaihin malamin ya samu gurbin karatunsa na digiru na uku, wato Dakta (Phd) a Jami'ar Usman dan Fodiyo da ke Sakkwato.
5) Malaman da suka karantar dashi
Malamansa na ilimi sun hada da Sheikh Abdulaziz Ali al-Mustafa (mutumin kasar Masar), Malam Nuhu a unguwar Dandago wanda ya karantar dashi fikihun malikiyya da wadansu litafan hadisi, Malam Muhammad Shehu wanda ya koyar dashi Nahawu da sarfu, da Balaga da kuma adab.
Sauran malaman kuma sun hada da Sheikh Jibrin Abubakar, da kuma Dr. Ahmad Muhammad Ibrahim daga Jami'ar Bayero ta Kano, sai kuma Sheikh Abdurrafi'u da Dr. Khalid Assabt.
6) Wasu daga cikin dalibansa
Wasu daga cikin dalibansa sun hada da Malam Rabi'u Umar Rijiyan Lemo, Malam Sani Abdullahi Alhamidi Dorayi, Abdullahi Usman, Malam Usman Sani Haruna da Ibrahim Abdullahi Sani. Sauran sun hada da Malam Yunus Ali Muhammad, Dr Salisu Shehu, Malam Shehu Hamisu Kura da Muhammad Madabo.
7. Litaffan da shaihun malamin ya koyar
Wasu daga cikin karatuttukan da Sheikh Ja'afar ya yi sun hada da tafsirin Alkura'ani mai girma, kitabu-tauhid, Umdatul Ahkaam, Arba'una Hadith, Kashfussahubuhaat, Bulugul Maraam, Riyaadussalihin, Siratun Nabiy, Ahkaamul Janaaiz da Siffatus-salatun nabiy.
8. Rubuce-rubucensa
Kafin rasuwarsa, marigayi Sheikh Ja'afar ya fara gagarumin aikin rubuta tafsirinsa a harshen Hausa a karkashin wata cibiya mai suna Cibiyar adana bayannai ta Sheikh Ja'afar.
9. Iyali
Shaihun malamin ya rasu ya bar matan aure biyu, da 'yaya 6 kuma daga bisani aka haifa masa na 7 kwanaki 58 bayan rasuwar sa.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng