Masana sunyi gargadi kan illolin amfani da wayyar salula da daddare ga dalibai
- Masana sunyi gargadi kan matsalolin da amfani da wayar salula cikin dare ke haifar wa dalibai musamman yara
- Musanan sun ce akwai wata shudin haske da ke fita daga fuskar wayar da ke jinkirta sinadarin da ke haddasa barci a jinkin dan adam
- Shi kuma rashin barcin yana haifar da matsaloli da yawa kamar saurin fushi, damuwa da rashin samun natsuwa
Amfani da wayar salula da sauran na'urorin hannu da dadare yana daburta yanayin barcin dalibai da kuma yin lahani ga lafiyar kwakwalwarsu inji masu nazarin ilimi na kasar Australia.
A sanarwar da ta bayar yau Juma'a, shugaban kungiyar shugabanin makarantu na Australia (ACT), Liz Bobos tace yawan amfani da wayar salula da dalibai keyi yakan canja halayen su inda basu iya barci da dadare sai dai da rana.
DUBA WANNAN: An damke wani dan shekaru 22 da laifin yiwa yar shekara 13 fyade
Bobos ta kara da cewa an samu karin adadin yara da ake turawa wajen likitoci masu nazarin halayan dan adam sosai duk da cewa yawancin tsare-tsaren lafiyar kwakwalwa basu duba yara wanda shekarunsu yayi kasa da 12.
Direktan Cibiyar nazarin mahimmancin barci ga Ilimi, Sarah Blunden tace hasken mai launin shudi da ke fita daga wayar salula ne ke jinkirta samuwar sinadarin dake kula da yadda dan adam ke barci wanda hakan ke canja yanayin da mutum ke barci.
Ta kuma kara da cewa da zarar yanayin barcin mutum ya samu tangarda, hakan na iya haifar da wasu matsalolin da yawa wanda suka hada da saurin fushi, damuwa da rashin samun natsuwa.
Bobos ta shawarci iyayen yara su sanya idanu kan yadda yaransu ke amfani da wayyar salula da sauran na'urorin hannu don su tabbatar na'urorin basu lahani ga rayuwar yaransu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng