Ana tare: Babban hafsan Sojan kasa, Buratai ya jaddada biyayyarsa ga shugaba Buhari

Ana tare: Babban hafsan Sojan kasa, Buratai ya jaddada biyayyarsa ga shugaba Buhari

Babban hafsan Sojan kasa, Laftanar janar Tukur Yusuf Buratai ya jaddada goyon bayan rundunar Soji tare da yin biyayya ga shugaban kasa Muhammadu Buhari, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Buratai ya bayyana haka ne a ranar Alhamis 12 ga watan Afrilu, a yayin rufe taron kara ma juna sani da babban hafsan Sojan ya shirya ma manyan Sojoji a babban birnin tarayya Abuja.

KU KARANTA: Jarabawar gwaji: Cikin Malaman makarantun sakandari a jihar Kaduna ya duri ruwa

Buratai ya samu wakilcin Manjo janar Rasheed Yusuf, shugaban tsare tsare na rundunar, inda yace a shirye Sojoji suke su hada karfi da karfe da sauran hukumomin tsaro don tabbatar da zaman lafiya a Najeriya.

Ana tare: Babban hafsan Sojan kasa, Buratai ya jaddada biyayyarsa ga shugaba Buhari
Buhari da Buratai

Bugu da kari Buratai ya tabbatar da cewa Sojoji ba zasu shiga cikin rikicin siyasa ba, don haka zasu cigaba da kokarin ganin sun kawo karshen matsalolin tsaro a Najeriya.

“Ina bada tabbacin zamu cigaba da girmama mutuncin dan Adam, tare da hakkokin dan Adam, a kokarinmu na kakkabe ayyukan miyagu a Najeriya, mun gano kalubalen da Sojoji ke fuskanta a ayyukan tsaro na musamman da muka kaddamar, kuma zamu mayar da hankulanmu akansu.” Inji shi.

Buratai a yayin taron ya kaddamar da wasu ka’idojin Soji guda uku, da suka kunshi ka’idar yaki da fafatawa, da kuma na kama mai laifi, rike shi da kuma yi masa tambayoyi.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel