Yanzu Yanzu: Buhari yayi ta’aziyya ga kasar Algeria kan hatsarin jirgin sama da ya kashe mutane 257

Yanzu Yanzu: Buhari yayi ta’aziyya ga kasar Algeria kan hatsarin jirgin sama da ya kashe mutane 257

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya aika sakon ta’aziyya ga gwamnatin kasar Algeria bisa ga babban rashi da tayi na mutuwar mutane 257 sakamakon hatsarin jirgin sama.

Haka zalika shugaban kasar ya mika sakon gaisuwa da tausayawa ga iyalan wadanda abun ya shafa.

Daga karshe yayi addu'an Allah ya sa masu dauriya da dangana.

Babban mai ba shugaban kasa shawara a kafofin watsa labarai, Garba Shehu ne ya wallafa a shafinsa na twitter.

KU KARANTA KUMA: Dalilin bayyana kudirina na tsayawa takara kafin tafiyata Ingila – Shugaba Buhari

Ya rubuta kamar haka: "A madadin gwamnati da mutanen kasar Najeriya, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya mika ta’aziyya ga shugaba Abdelaziz Bouteflika da mutanen Algeria kan hatsarin jirgin saman sojoji day a afku a ranar Laraba a kusa da filin jirgin sama na Boufarik a Algeria wanda yayi sanadiyan rasa rayuka da dama.

"Shugaban kasar ya kuma mika ta’aziyya ga iyalai da abokan wadanda abun ya shafa da sauran kasashe wanda suka shiga alhini sakamakon abun bakin cikin."

Idan bazaku manta ba a ranar Laraba, 11 ga watan Afrilu ne jirgin saman sojin kasar Algeriya dauke da mutane 257 yayi hatsari, inda dukkan mutanen ciki suka mutu.

Legit.ng ta kawo cewa mafi akasarinsu sojoji ne da iyalansu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel