Yanda farashin Fetur, Kalanzir, da Gas suka fadi a watan Maris

Yanda farashin Fetur, Kalanzir, da Gas suka fadi a watan Maris

- Rahoto ya nuna cewa kudin da masu aiki da kalanzir a gida suke siyan duk lita ya fadi da kaso 6.79 a cikin dari a wata wata Kuma da kaso 13.66 a cikin dari a duk shekara shekara zuwa N268.99 a watan Maris daga N288.57 a watan fabrairu na wannan shekarar

Yanda farashin Fetur, Kalanzir, da Gas suka fadi a watan Maris

Yanda farashin Fetur, Kalanzir, da Gas suka fadi a watan Maris

Farashin kalanzir da gas din girki ya fadi a watan Maris, kamar yanda National Bureau of Statistics ta ruwaito a jiya.

Rahoto ya nuna cewa kudin da masu aiki da kalanzir a gida suke siyan duk lita ya fadi da kaso 6.79 a cikin dari a wata wata Kuma da kaso 13.66 a cikin dari a duk shekara shekara zuwa N268.99 a watan Maris daga N288.57 a watan fabrairu na wannan shekarar.

DUBA WANNAN: Wani Minista ya bukaci a fara kiran Sallah da Whatsapp a Ghana

Ittifakin ya nuna cewa jihohin da ke da tsadar kalanzir din sune Nasarawa( N306.07), Yobe (N300.78) da kuma Cross River (N300.68). Jihohi kuma masu arhar kalanzir din sune Abia (N229.35),Delta (N227.77) da Borno (N225.13).

Haka ma kuma, farashin kalanzir na galan galan na faduwa da kaso 8.45 a cikin dari a duk wata da kuma kaso 19.57 a cikin dari duk shekara zuwa N943.27 a watan Maris daga N1,030.33 a watan fabrairu na shekarar nan.

Rahoton ya nuna jihohin da suka fi tsadar galan din kalanzir din, su ne kebbi (N1105.00),Benue(N1096.67) da Jigawa (N1061.90). Sai kuma jihohin da sukafi arhar galan din kalanzir din sune Ebonyi (N828.57),Delta (N821.54) da kuma Rivers(N814.08).

Haka shima farashin cika kilogram 5 na gas din girki ya fadi da kaso 3.03 cikin dari a wata wata da kuma kashi 16.16 a cikin dari a duk shekara zuwa N2090.97 a watan Maris daga N2155.97 a watan fabrairu na wannan shekarar.

Jihohi masu tsadar gas din girki sune Borno (N2487.50), Yobe (N2500.00) da Bauchi (N2400.00) suke siyarda 5kg na gas din.

Jihohin da suke da arhar gas din sune Abuja (N1,760.00), Ebonyi (N1,870.00) da kuma Ekiti (N1,895.00).

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel