Jarabawar gwaji: Cikin Malaman makarantun sakandari a jihar Kaduna ya duri ruwa
Malaman makarantun sakandarin gwamnati a jihar Kaduna sun shiga halin ni yasu biyo bayan tabbatuwan gudanar da jarabawar gwaji da gwamnatin jihar Kaduna ta dauki gabarar shiryawa.
Daily Trust ta ruwaito gwamnan jihar, Nasir Ahmad El-Rufai ya bayyana cewa nan bada dadewa ba zasu shirya ma Malaman jarabawar gwaji, don tantance aya da tsakuwa a tsakanin Malaman, kamar yadda aka yi ma Malaman Firamari.
KU KARANTA: Kwana yazo karshe: Wani dan jariri ya mutum bayan ya tunjuma cikin randar ruwa a dakin babarsa
Majiyar Legit.ng ta ruwaito a cikin jarabawar da aka shirya ma Malaman makarantun Firamari su 30,000, kimanin 21,780 sun gaza samun kashi 70 cikin 100 na makin da gwamnatin ta sanya.
Tuni dai gwamnatin jihar ta maye gurbin gurbatattun Malaman da sabbin Malamai da gwamnatin ke ganin sun fi cancanta, su 15,000, inda nan bada dadewa ba kuma zata dauki cikon 10,000, kamar yadda ta alkarwanta daukan Malamai 25,000.
Sai dai a yayin da ake tsimayin ranar zana jarabawan gwaji na Malaman Sakandarin, cikin wasu Malaman ya duri ruwa, yayin da wasu kuwa suka ce ko dar basu ji ba, kamar yadda wani Malami dake koyarwa a Zaria ya bayyana, inda yace ta hanyar gwada kwarewar Malamai a wajen koyarwa ne kadai za’a ya gane kwararren Malamai.
“Abin ya kamata su gwada Malamai a kai kenan, bai kamata a gwada Malamin Turanci ilimin tattalin arziki ba ko makamancn haka, matukar aka yi amfani da irin gwajin da aka yi ma Malaman Firamari, tabbas hakan ba zai fidda A’I daga rogo ba.” Inji Malamin.
Wani Malamin kuma ya shawarci gwamnati ta dauki hukumomin da suke kula da Malamai wajen shirya jarabawar, hakazalika yayi kira da a sanya maki mai tsaka tsakiya. Wata Malamar kuma nuna adawa ta yi da jarabawar “Bana son jarabawar, bana so ayi ta.”
Su ma shuwagabannin kungiyoyin kwadago da kungiyar Malamai sun goyi bayan jarabawar, sai dai sun yi kira da gwamnati ta mika ragamar shirya jarabawar ga hukumar rajistan Malamai, kamar yadda shugaban kungiyar Malaman jihar Audu Kamba ya bayyana, inda yace hakan ne kadai zai tabbatar da adalci a jarabawar.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng