Yaran El-Rufai ne – Inji wasu Yan fashi yayin da suka tare sabbin Malamai 15 da Gwamnati ta dauka

Yaran El-Rufai ne – Inji wasu Yan fashi yayin da suka tare sabbin Malamai 15 da Gwamnati ta dauka

Wasu sababbin Malamai su 15 da gwamnatin jihar Kaduna ta dauka a yan kwanakin nan, kuma ta tura su karamar hukumar Birnin Gwaro da nufin koyarwa a makarantun Firamarin garin sun gamu da yan fashi da makami, inji rahoton Daily Trust.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito yan fashin sun tare Malaman ne a daidai kauyen Dogon Dawa dake karamar hukumar Birnin Gwari, inda aka tura su makarantar Firamarin kauyen don su koyar.

KU KARANTA: 2019: Sule Lamido ya tafi neman tabarraki a wajen IBB a wata ziyara da ya kai masa (Hotuna)

Daya daga cikin Malaman ya bayyana cewa sai da suka fara yada zango a ofishin hukumar ilimin firamari ta jihar Kaduna dake garin Birnin Gwari, inda suka bada sunayensu, kimanin su 24 a matsayin sabbin Malaman da aka tura, daga nan kuma suka dauki motocin Golf guda 3, don su karasa da su Dogo Dawa.

Shi ma wani daga cikin Malaman mai suna Moses Joseph ya bayyana cewar kwata kwata basu yi tafiyar da ta kai mintuna goma ba, sai kwatsam suka cimma shingen yan fashi da makami, inda suka fitar dasu daga motocinsu, suka kwace musu kudade da wayoyi.

“Sun kwace wayoyinmu gaba daya, kudaden dake jikinmu, littafanmu, kai har ma sun tafi da takardun kammala karatun wani daga cikinmu, sun fara tambayarmu mu su waye, da muka fada musu, sai suka ce “Ah! Yaran El-Rufai ne”

Malam Joseph yace saura kiris da sun yi awon gaba da yan matan dace cikinsu, inda yace har sun waresu, amma daga bisani wani daga cikinsu ya bada shawarar a kyale yan matan. Daga nan yace sai dunguma zuwa Birnin Gwari, inda suka shaida ma Yansanda abinda ya faru.

Sai dai Malamin yace babu wanda zai koma kauyen nan da sunan zuwa koyarwa, sai dai su rasa aikin.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng