Barayin shanu dauke da muggan makamai sun kai hari a jihar Kaduna, sun jikkata mutane 3

Barayin shanu dauke da muggan makamai sun kai hari a jihar Kaduna, sun jikkata mutane 3

Wasu yan bindiga daga dazukan dake makwabtaka da jihar Kaduna sun kai wani hari a karamar hukumar Birnin Gwar na jihar Kaduna, inda suka jikkata mutane guda uku, inji rahoton BBC Hausa.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito yan bindigan sun kai wannan farmaki ne a ranar Talata 10 ga watan Afrilu a kauyukan Layin Lasan da Layin Nakurmi, inda suka bude ma jama’an garin wuta, a sanadiyyar haka mutane uku suka jikkata daga harbin bindiga.

KU KARANTA: Yan Najeriya sun gudanar da zanga zangar nuna adawa da Tazarcen Buhari

Wani dan garin ya bayyana cewa: “Yan bindiga da dama ne suka dira kauyenmu akan Babura dauke da bindigu da dama kirar AK 47, inda suke bude wuta a wani hari irin na mai kan uwa da wabi.”

Sai dai majiyar ta kara da cewa jami’an tsaro sun samu nasarar fatattakar yan bindigar gaba dayansu, inda suka tsere zuwa dajin Hamada, dake cikin karamar hukumar Sabuwa ta jihar Katsina.

Idan za’a tuna a watan data gabata ne dai wasu yan bindiga, yaran tsohon shugaban yan bindigar jihar Zamfara, Buharin Daji suka kai wani mummunan hari a karamar hukumar Birnin Gwari, inda suka kashe Sojoji goma sha daya.

Ayyukan yan bindiga ya cigaba da ruruwa ne dai tun bayan da aka kashe Buharin Daji, wanda ya gamu da ajalinsa a hannun wani tsohon yaronsa, mai suna Dogo Gide, a sakamakon haka yan bindiga sun yi ta kai munanan hare hare a jihohin Zamfara da Kaduna.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel